Afghanistan

Yarjejeniyar sulhu tsakaninmu da Taliban ta rushe - Ghani

Wani sojan Afghanistan bayan ceto daya daga cikin jariran da harin 'yan ta'adda ya rutsa da su a babban asibitin Kabul, babban birnin Afghanistan. 12/05/2020.
Wani sojan Afghanistan bayan ceto daya daga cikin jariran da harin 'yan ta'adda ya rutsa da su a babban asibitin Kabul, babban birnin Afghanistan. 12/05/2020. Reuters video image

Shugaban Afghanistan Ashraf Ghani, ya bai wa jami’an tsaron kasar umarnin sake kaddamar da farmaki kan mayakan Taliban bayanda magoya bayan kungiyar suka tsananta hare-hare tare da kashe mutane da dama cikin ‘yan kwanakin nan.

Talla

A jiya talata, wasu ‘yan bindiga suka afkawa wani asibiti da ke birnin Kabul, inda suka kashe mutane da dama ciki har da jarirai a asibitin, lamarin da yasa shugaban ya zargi kungiyar Taliban da karya yarjejeniyar tsagaita wuta da bangarorin biyu suka sanyawa hannu watanni biyu da suka gabata.

Ma'aikatar cikin gidan Afghanistan ta ce jami'an tsaron kasar sun yi nasarar kashe ‘yan bindiga ukun da suka shafe tsawon awanni suna barin wuta kan babban asibitin kasar dake birnin Kabul.

Kakakin ma'aikatar cikin gidan Tareq Arian, ya ce lamarin ya rutsa da iyaye, jarirai da kuma jami'an kiwon lafiya, inda hoton bidiyo ya nuna jami'an tsaro na fito da jarirai daga harabar asibitin jina-jina.

Mista Tariq ya ce an yi nasarar ceto sama da mutane 100, cikinsu har da baki yan kasashen waje 3, bayaga mutane 15 da suka jikkata a asibitin dake samun tallafi daga kungiyar likitoci ta kasa da kasa MSF.

Saidai kusan awa guda da harin Kabul, kakakin rundunar 'yan sandan gabashin lardin Nangarhar, Ayatullah Khogyani ya ce wani dan kunar bakin wake ya hallaka mutane 24, yayin gudanar da jana'izar shugaban rundunar 'yan sandan wannan yanki.

Kakin ‘yan sandan ya ce dan kunar bakin waken ya tarwatsa bamabaman dake tattare da shi ne a tsakiyar gudanar da bikin jana'izar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.