Duniya-China

China ta sha alwashin wadata kasashen duniya da riga-kafin coronavirus

Shugaban China Xi Jinping.
Shugaban China Xi Jinping. REUTERS/Maxim Shemetov

Gwamnatin China ta bayyana aniyar sakin riga-kafin cutar coronavirus domin amfanin al’ummar duniya da zarar ta kammala gwajin riga-kafin a dakunanta na binciken kimiya.

Talla

Shugaban China Xi Jinping ya bayyana haka a yayin gabatar da jawabi a zauren Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya.

Yanzu haka kasar China na da nau’ukan riga-kafin coronavirus har guda biyar da ake gwajinsu a dakin binciken kimiya a daidai lokacin da kasashen duniya ke rige-rigen dakatar da kwayar cutar, wadda ta kashe sama da mutane dubu 316 a sassan duniya.

Shugaba Xi ya ce, samar da riga-kafin annobar, zai kasance gudunmawar China ga kasashe masu tasowa da ake ganin za su samu riga-kafin cikin sauki.

Shubagaban na China ya kuma shaida wa zauren Hukumar Lafiyar ta Duniyar cewa, kasarsa za ta bada tallafin dala biliyan 2 cikin shekaru biyu domin yaki da COVID-19.

A bangare guda, kwararru a fannin kiwon lafiya sun ce, za a dauki a kalla watanni 12 zuwa 18 koma fiye da haka, kafin samar da ingantacen riga-kafin cutar coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.