China

China ta sanar da kawo karshen annobar coronavirus

Wasu 'yan kasar China a babban birnin kasar Beijing. 6/4/2020
Wasu 'yan kasar China a babban birnin kasar Beijing. 6/4/2020 © REUTERS/Tingshu Wang

Ma’aikatar lafiyar China ta sanar da cewa babu wanda ya kamu da cutar coronavirus a fadin kasar yau Asabar.

Talla

Karo na farko kenan da aka wayi gari a kasar ba tare da annobar ta shafi kowa ba, tun bayanda tayi karfi a watan Janairun wannan shekara, bayan bulla a birnin Wuhan cikin Disambar bara.

Sanarwar ma’aikatar lafiyar ta China na zuwa kwana guda, bayanda Fira Ministan kasar Li Keqiang ya yi shelar samun nasarar kawo karshen annobar ta coronavirus a yayin babban taron kasar dake gudana.

Kawo yanzu dai mutane dubu 4 da 634 cutar ta halaka a China, daga cikin dubu 82 da 971 da suka kamu, yayinda kuma dubu 78 da 258 suka warke.

Kasa da makwanni biyu da suka gabata, shugaban Amurka Donald Trump, yace ba ya fatan sake yin magana da takwaransa na China Xi Jinping inda a fakaice ma yake cewa abu ne mai yiwuwa ya yanke duk wata alaka da kasar ta China, saboda takun sakar da kasashen ke yi da juna dangane da batun Coronavirus.

Trump ya share makwanni yana tuhumar China da kirkirar cutar coronavirus daga dakin gwaje-gwajenta a birnin Wuhan, duk da cewa kasar ta China na cigaba da musanta zargin, zalika binciken tawagar kwararrun hukumomin leken asirin Amurka ya nuna cewa, babu hannun dan adam wajen kirkirar cutar ko kuma sauya mata halitta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.