India

Farin dangon da ka iya cinye mutum dubu 35 a lokaci guda sun kacalcala gonaki a India

Wani bangare na miliyoyin farin dangon dake afkawa gonaki a sassan duniya.
Wani bangare na miliyoyin farin dangon dake afkawa gonaki a sassan duniya. Caribbean National Weekly

Dimbin farin-dango da adadinsu ya haura miliyan 200 na lalata albarkatun gona a sassan Yammaci da kuma Tsakiyar kasar India, lamarin da ya sa hukumomi suka zage damtse wajen magance iftila’in, mafi muni a kasar cikin shekaru 30 da suka gabata.

Talla

Hukumomin na India sun tura jirage marasa matuki da tantan da kuma kananan motoci domin gano wadannan farin-dangon tare da feshe su da magungunan kashe kwari.

Sai dai tuni farin suka lalata kusan kadada dubu 50 a gonaki, yayinda gwamnatin India ta ce, ana samun tawaga-tawaga na farin daga takwas zuwa 10 a wasu yankuna na Rajasthan da Madhya Pradesh.

Barnar da farin suka yi na zuwa ne a daidai lokacin da manoman kasar ta India ke kokarin murmurewa daga illar da annobar coronavirus ta yiwa ayyukansu ta noma.

Ko a cikin watan Afrilun da ya gabata, sai da wadannan fari suka kacalcala gonaki a Pakistan mai makwabtaka da India, kafin daga bisani su kutsa cikin Rajasthan.

Hukumar Samar da Abinci da Bunkasa Ayyukan Gona ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce, fari miliyan 40, za su iya cinye mutane dubu 35 a matsayin abincinsu ko kuma giwaye har guda shida.

Kididdigar masana kuma tace a cikin kowace tawaga guda ta farin dangon da a turance ake kira da ‘swarm’ adadin farin na iya kaiwa miliyan 80

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.