Iran

Mutane 225 suka mutu a zanga-zangar adawa da karin farashin mai - Iran

Daya daga cikin bankunan da masu zanga-zangar adawa da karin farashin man fetur a Iran suka kone a ranar 20 ga watan Nuwamban shekarar 2019.
Daya daga cikin bankunan da masu zanga-zangar adawa da karin farashin man fetur a Iran suka kone a ranar 20 ga watan Nuwamban shekarar 2019. Reuters

Ma’aikatar cikin gidan Iran ta ce mutane 225 suka mutu a kasar yayin zanga-zangar adawa da karin farashin man fetur cikin watan Nuwamban shekarar da ta gabata.

Talla

Sanarwar na zuwa ne bayan rahoton da kungiyar Amnesty International ta wallafa, da ya ce adadin Iraniyawan da suka rasa rayukan nasu ya haura 300, yayin zanga-zangar adawa da gwamnatin, yayinda Amurka tace akalla mutane dubu 1 jami’an tsaron Iran suka halaka.

Ranar 15 ga watan Nuwamban bara, dubban ‘yan Iran suka soma zanga-zangar adawa da karin farashin man fetur da gwamnati tayi a birnin Teheran, wadda daga bisani ta bazu zuwa wasu biranen akalla 100, inda aka kone gidajen mai masu yawan gaske, da kuma kaiwa ofisoshin ‘yan sanda farmaki, kafin daga bisani jami’an tsaron su yi amfani da karfi wajen kawo karshen boren.

A waccan lokacin dai Iran ta zargi Amurka, Isra’ila da kuma Saudiya da hannu wajen haddasa boren da aka yi, da nufin haddasa rashin zaman lafiya a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI