Coronavirus

'Babu wanda ya kubuta daga coronavirus a duniya'

Shugaban Gamayyar Samar da Riga-kafi ta Duniya ya gargadi cewa, babu wani bil’adama da ya tsira daga sabuwar cutar coronavirus har sai an samu maganinta, yayin da ya bukaci hadin kan kasashen duniya gabanin taron samar da kudin yaki da cutukan da aka yi biris da su sakamakon zuwan Covid-19.

Coronavirus ta yi duniya mummunar damka
Coronavirus ta yi duniya mummunar damka indiatimes
Talla

Masana kimiya na rige-rigen gano hakikakin riga-kafin cutar Covid-19 a daidai lokacin da kasashen duniya ke fafutukar farfado da tattalin arzikinsu wanda ya durkushe sakamakon matakan killace jama’a a gidajensu don hana yaduwar cutar.

Shugaban Gamayyar Samar da Riga-kafi ta Duniya, Seth Berkley ya ce, dole ne kasashen duniya su tabbatar cewa, al’umominsu sun samu damar karbar duk wani riga-kafin da za a samar nan gaba ba tare da la’akari da arziki ko kuma talaucinsu ba.

Berkley na magana ne gabanin taron da Birtaniya za ta karbi bakwancinsa ta kafar bidiyo a gobe Alhamis, inda gamayyar samar da riga-kafin ke fatan tara a kalla Dala biliyan 7.4 domin ci gaba da shirin samar da riga-kafin cutukan da suka hada da Kyanda da Shan-Inna da Zazzabin Typhoid da aka yi biris da su saboda zuwan annobar coronavirus.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da coronavirus ta yi sanadin ajalin mutane dubu 380 da 428 a sassan duniya tun bayan bullarta a karshen shekarar bara a China.

Yanzu haka mamatan da coronavirus ta aika lahira a Brazil kadai sun zarce dubu 30, abin da ya sa kasar ta zama ta hudu a duniya da wannan annoba ta fi yi wa ta’annati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI