Hong Kong

Ana zanga-zangar Tiananmen a Hong Kong

Masu taron addu'oin tunawa da mutanen da aka murkushe a boren Tiananmen
Masu taron addu'oin tunawa da mutanen da aka murkushe a boren Tiananmen REUTERS/Jason Lee

Dubban mutane rike da kyandir sun gudanar da zanga-zanga a sassan Hong Kong domin tunawa da zagayowar ranar da mahukuntan China suka yi amfani da karfi wajen murkushe masu zanga-zangar Tiananmen da aka gudanar shekaru 31 da suka gabata.

Talla

Dubban masu zanga-zangar sun fantsama kan tituna duk da cewa, akwai dokar haramta taruwar jama’a , yayin da ake dari-darin kazancewar boren saboda wani shirin samar da sabuwar dokar tsaro a yankin na Hong Kong.

Masu boren sun yi dandazo a dandalin Victoria wanda a cikinsa ne aka saba gudanar da tarukan addu’oin dare duk shekara don tunawa da mutanen da suka mutu a boren na Tiananmen.

Sai dai an samu ‘yar karamar hatsaniya a wasu yankuna cike da manyan shaguna, yayin da jami’an ‘yan sanda suka cafke masu tayar da kura a ire-iren wadannan wurare.

Kodayake ‘yan sandan sun nuna halin ko in kula da masu gudanar da boren lumana.

Zanga-zangar ta yau na zauwa ne ‘yan sa’o’i bayan ‘yan Majalisun Dokokin Hong Kong sun amince da kudirin dokar da ya bada damar hukunta duk wanda aka samu da laifin isgilanci ga taken kasar China.

Masu zanga-zangar rajin kare demokradiya na kallon wannan sabuwar doka a matsayin wani bangare na take ‘yancin jama’ar Hong Kong.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI