Iran

Iran za ta aiwatar da hukuncin kisa kan wanda ya taimaka wa Amurka wajen kashe Soleimani

Shugaban kasar Iran Hassan Rohani tare da Marigayi Qassem Soleimani, babban kwamandan Sojin kasar.
Shugaban kasar Iran Hassan Rohani tare da Marigayi Qassem Soleimani, babban kwamandan Sojin kasar. REUTERS/Brendan McDermid

Iran ta ce lalai za ta aiwatar da hukuncin kisa kan Bafarisen nan da ya taimaka wa Amurka da leken asirin da ya kai ga kisan babban janar din sojin nan na ta, bayan kotun koli ta jaddada hukuncin da aka mai tun da farko.

Talla

An yanke wa Mahmoud Mousavi Majd hukunci ne bisa laifin yin leken asiri kan sojin Iran, lamarin da ya kai ga kisan Janar Qasem Soleimani da Amurka ta yi ta wajen amfani da jirgi mai sarrafa kansa.

An sami Majd da laifin karbar wasu makudan kudade daga hukumar leken asiri na Amurka CIA, da ta Isra’ila Mossad, a cewar wata sanarwa daga ma’aikatar tsaron Iran.

Ma’aikatar tsaron Iran din ta ce kotun koli ta jaddada hunkuncin da aka yanke wa Majd, kuma nan ba da jimawa ba za ta aiwatar da shi.

Soleimani ne kwamandan dakarun Quds, wani bangare na rundunar juyin juye hali na Iran, wato Iran Revelutionary Guards, kuma Amurka ta kashe shi a kusa da filin tashi d saukar jiragen sama na birnin Bagadaza a watan Janairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.