China-Coronavirus

Corona ta sake bulla a birnin Pekin na kasar China.

Wasu mata 2 sun shige rigunan kariya a kusa da kasuwar  Xinfadi, inda aka sake samun bullar cutar a Pékin, 13 yuni 2020.
Wasu mata 2 sun shige rigunan kariya a kusa da kasuwar Xinfadi, inda aka sake samun bullar cutar a Pékin, 13 yuni 2020. GREG BAKER / AFP

A yayin da mutane dubu 425  suka rasa rayukansu sanadiyar annobar cutar coronavirus a duniya, a yau assabar mahukumta Pekin na kasar China, sun bayyana  rufe wasu anguwanni 11, sakamakon sake gano bulur annobar ta coronavirus a wata kasuwa dake makwabtaka da su.

Talla

A cewar mahukumtan na china, an sake samun mutane 7 da su ka kamu cutar ne a kewayen kasuwar ta Xinfadi, 6 daga cikinsu kuma an gano su ne a safiyar yau assabar. Tuni dai aka rufe makarantun faramare da kuma na reno guda 9 dake yankin

A jimilce dai, tun ranar alhamis 11 ga watan Yuni kawo yau assabar 13 ga watan, kimanin mutane 51 aka sake gano sun kamu da cutar, 49 daga cikinsu kuma, dukkaninsu na da alaka da kasuwar ta Xinfadi ne, dake yankin kudancin birnin na Pekin. Daga cikin mutanen 49 da suka kamun kuma, 45 ba su nuna wata almar kamuwa da cutar ba a cewar hukumomin na lafiya.

Tun ranar alamis 11 ga watan yuni ne birnin na Pekin ya kaddamar da gwajin cutar ga kimanin mutane dubu 10,000.

Inda kowo safiyar assabar 13 ga watan, mahukumtan suka ce, mutane dari 500 aka gudanar da gwajin a kansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.