Asiya

Rikici ya kaure tsakanin China da India

Gwamnatin kasar India tace sojojin ta 20 sun rasa rayukan su a aranagmar da suka yi da takwarorin su na China akan iyakar dake tsakanin su, sakamakon rikici kan mallakar wani yanki na Himalaya.

Yankin Himalaya da China da India suke takkadama a kai
Yankin Himalaya da China da India suke takkadama a kai AFP/Tauseef Mustafa
Talla

Da farko India tace sojojin ta 3 suka mutu sakamakon arangamar, yayin da daga bisani tace adadin ya tashi zuwa 20 sakamakon mutuwar Karin mutane 17 daga cikin su.

Ya zuwa yanzu dai China bata bada adadin nata sojin da suka mutu ba, amma rahotanni an samu rasa rayuka daga nata bangaren.

An kwashe dogon lokaci ana rikici kan mallakar yankunan dake iyakar kasashen biyu, ciki harda yakin da kasashen biyu suka fafata a shekarar 1962.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI