India-China

China da India sun kama hanyar dinke barakarsu

Firaministan India ya ce, rayukan sojojin kasar ba za su tafi a banza ba
Firaministan India ya ce, rayukan sojojin kasar ba za su tafi a banza ba REUTERS/Adnan Abidi

Manyan jami’an kasashen India da China sun gudanar da wani taro domin sasanta rikicin da ya yi sanadin mutuwar sojojin India 20 akan iyakar da ke tsakaninsu, yayin da Firaminista Narendra Modi ke cewa rayukan sojojin ba za su tafi a banza ba.

Talla

Ministocin Harkokin Wajen India da na China, Subrahmamyan Jaishankar da Wang Yi sun tattauna a tsakaninsu ta waya, domin kwantar da hankalin kasashen biyu sakamakon tashin hankalin da aka samu jiya.

Hukumomin India sun tabbatar da kashe musu sojoji 20 a arangamar da aka yi jiya, amma China ta ki bayyana komai dangane da nata sojin da suka jikkata, amma wasu majiyoyi na cewa a kalla sojojinta 40 suka mutu ko kuma suka samu raunuka.

Ma’aikatar Harkokin Wajen China ta bukaci India da ta gudanar da bincike kan abinda ya haifar da tashin hankalin da zummar hukunta wadanda aka samu da laifi.

Ministan Harkokin Wajen China ya gargadi Indian kan cewa, kada ta yi sako-sako da lamarin ko kuma ta raina irin matakin da China ka iya dauka domin kare yankinta.

Shi kuwa Firaminista Narendra Modi ya sha alwashin cewar rayukan sojin kasar da aka kashe ba za su tafi a banza ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.