China

Cutar COVID-19 ta sake barkewa a birnin Beijing na China

Wasu mazauna birnin Beijing na China karkashin matakan dakile COVID-19.
Wasu mazauna birnin Beijing na China karkashin matakan dakile COVID-19. © REUTERS/Tingshu Wang

China ta sanar da rufe wasu tashoshin jiragen sama da kuma soke tashin jirage sama da 1,200 a Beijing tare da rufe makarantu a yunkurin dakile annobar COVID-19 da ta sake barkewa a birnin.

Talla

Rahotanni sun ce sabbin mutane 31 aka samu dauke da cutar a jiya laraba, yayin da hukumomi suka bukaci mazauna birnin da su kaucewa barin garin, yayin da ake cigaba da fargabar sake yaduwar cutar.

Ana zargin cewar an sake samun barkewar cutar ce daga wata kasuwar kayan abinci da ke Xinfadi, yayin da aka killace mazauan wasu yankuna.

Tun farko dai cutar ta COVID-19 ta samo asali ne daga yankin Wuhan na tsakiyar China inda aka samu barkewarta a karshen watan Disamban bara, wadda kuma tuni ta fantsamu ilahirin kasashen duniya tare da kashe mutane kusan dubu dari 5.

Masana dai sun yi imanin cewa cutar an samo ta ne daga ko dai jikin Jemage ko kuma Maciji nau'in dabbobin da dukkaninsu ke matsayin abinci ga al'ummar kasar ta China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.