China za ta gabatar da wasu yan Canada gaban kotu
Wallafawa ranar:
China ta ce, ta fara shari’ar wasu ‘yan kasar Canada biyu da ta tsare tun a watan Disambar 2018, ana zargin su da leken asiri.Cigaba da rike wadanan mutane kan iya kara rura wutan rikici tsakanin hukumomin Bejin da Ottawa.
A kasar ta China babban mai gabatar da kara na gwamnati, ya ce mutanen biyu, tsohon jami’an diflomasiya ne, Michael Kovrig da dan kasuwa Michael Spavor duk zasu fuskanci shari’a kan zargin leken asiri da kuma fallasa bayanan sirri.
Tsawon shekaru kasar ta China ta karfafa matakan tsaro wata hanyar kare bayanan sirrin kasar daga masu farautar haka daga kasashen waje.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu