Asiya

Fiye da yara miliyan 100 coronavirus ta jefa cikin talauci a Asiya- MDD

Wasu yaran kabilar Hui marasa rinjaye a China.
Wasu yaran kabilar Hui marasa rinjaye a China. REUTERS/Stringer

Majalisar Dinkin Duniya ta ce annobar coronavirus ta jefa akalla yara sama da miliyan 100 a yankin Kudancin Asia cikin talauci sakamakon yadda cutar ta shafi tattalin arzikin yankin.

Talla

Daraktan Hukumar da ke kula da Yankin Jean Gough ya ce matsalar ta shafi yin rigakafin cuttutuka da samar da abinci mai gina jiki da kayan more rayuwa, inda ya bukaci daukar matakan gaggawa domin rage radadin matsalar.

Yankin kudancin Asia na dauke da yara miliyan 600 da suka fito daga kasashen India da Pakistan da Afghanistan da Nepal da Bangladesh da Sri Lanka da Maldives da Bhutan, kuma miliyan 240 daga cikin su na fama da tsananin talauci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI