Asiya

Indonesia ta ceto wasu yan kabilar Rohingya a cikin teku

Wasu daga cikin yan Rohingya da aka ceto
Wasu daga cikin yan Rohingya da aka ceto REUTERS/Stringer

Hukumomin Indonesia sun ce sun ceto akalla Yan kabilar Rohingya 100 da suka fito daga Myanmar a cikin tekun dake kusa da tsibirin Sumatra, wadanda suka hada da yara 30 daga cikin su.

Talla

Shugaban hukumar tsaron teku a yankin Aceh, Muhammad Nasir yace an gano wadannan mutanen ne a cikin wani kwale kwale mara inganci suna yawo a saman ruwa, kafin masu kamun kifi su gano su.

Nasir yace mutanen sun kwashe kwanaki a cikin teku ba tare da abinci da ruwan sha ba.

Yan kabilar Rohingya dake fuskantar mawuyacin hali a Myanmar na barin kasar zuwa kasashen Malaysia ko Indonesia domin samun mafaka, yayin da dama daga cikin su kan mutu a teku.

Shugaban hukumar kare hakkin Bil Adama ta Amnesty Inrternational a Indonesia Usman Hamid ya bukaci taimakawa wadannan baki da suka kunshi mata da yara wadanda ke kwashe kwanaki a cikin teku ba tare da abinci ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI