Pakistan ta kori matuka jiragen samanta 150

Wani jirgin saman kasar Pakistan
Wani jirgin saman kasar Pakistan REUTERS/Faisal Mahmood

Jiragen Saman Pakistan dake zirga zirga a kasashen duniya, sun ce sun kori matukan su kashi daya bisa uku saboda binciken da ya gano cewar suna dauke ne da takardar kwarewa ko kuma lasisi na bogi, wata guda bayan wani hadarin da ya kashe mutane 98.

Talla

Mai Magana da yawun hukumar Abdullahi Hafeez Khan yace binciken da gwamnatin kasar ta gudanar a shekarar da ta gabata, ya bankado cewar matuka jiragen 150 daga cikin 434 basu da kwarewar tuka jirgi ko kuma sun biya kudi ne ta bayana fage domin samun lasisin.

Jami’in yace tuni aka dakatar da wadannan matuka 150, amma kuma a cikin su babu matuka biyun da suka samu hadari a jirgin da ya fadi a Karachi.

Ministan sufurin jiragen saman kasar Ghulam Sarwar Khan ya shaidawa Majalisar dokokin kasar cewar binciken gwamnati ya gano matuka jiragen 260 basu da takardar horo mai inganci daga cikin matuka jiragen 860 da ake da su a Pakistan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI