China

China ta hana mata daukar ciki don rage yawan Musulmai

Mata 'yan kabilar Uighur na fuskantar cin zarafin hana su haihuwa a Xianjing na China
Mata 'yan kabilar Uighur na fuskantar cin zarafin hana su haihuwa a Xianjing na China REUTERS/Petar Kujundzic

China na daukar tsauraran matakan tilasta wa ‘yan kabilar Uighur da wasu tsiraru rage haihuwa da zummar dakile yawan al’ummar Musulmi, yayin da a gefe guda, gwamnatin kasar ke karfafa wa ‘yan kabilar Han guiwar ci gaba da haihuwa.

Talla

A can baya, daidaikun mata sun yi korafi game da tilasta musu takaita haihuwa, kuma wannan tilastawar ta dada tsananta a yanzu kamar yadda binciken Kamfanin Dillancin Labaran AP ya nuna.

AP ya tattara alkalumansa ta hanyar amfani da kididdigar hukumomi da wasu bayanai na gwamnati da hirarrakin da ya yi da mutanen da aka tsare su a wani sansani saboda kin bin tsarin rage haihuwar.

Wasu masana sun bayyana wannan matakin na hana haihuwar da gwamnatin China ta fara aiwatarwa fiye da shekaru hudu a yankin Yammacin Xinjiang mai nesa, a matsayin wani nau’i na kisan kare dangi.

Gwamnatin Xinjiang na tilasta wa matan da suka fito daga tsirarun kabilu gudanar da gwajin juna-biyu akai-akai kuma tana matsa wa dubban mata zubar da ciki ko kuma ta cusa musu tsinadaran hana daukar ciki a mahaifarsu kamar yadda alkaluman da AP ya tattara suka nuna.

Gwamnatin ta Xinjiang na garkame tare da azabtar da mutanen da suka ki bin tsarin takaita haihuwar kamar yadda AP ya bankado.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.