Haramun ne mamaye yankunan Falasdinawa - MDD

Wasu Falasdinawa yayin zanga-zangar nuna adawar mamayan Isra'ila
Wasu Falasdinawa yayin zanga-zangar nuna adawar mamayan Isra'ila Mohammed Salem/Reuters

Shugaban Hukumar kare ‘Yancin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya Michelle Bachelet ta ce yunkurin da Israela ke yi na sake diban wani yankin a Yammacin gaban kogin Jordan ya haramta, kuma akwai hadarin gaske.

Talla

Gabanin aiwatarda ikirarin Israela na kamface yankin da take shirin aiwatarwa, Shugaban Hukumar kare ‘yancin dan adam na Majalisar Dinkin Duniya na bukatar ganin Faranministan Israela Benjamin Netanyahu ya jingine niyyar tasa.

Ta ce duk wani yunkuri na mamaye wani yankin haramtacce ne, koda kashe 305 ne ko kuma kashi 5% inda take bukatar Israela ta saurari abinda wasu manyanta da suka hada da janarorin sojinta da wasu dake sassan duniya dake hana yin dukkan mamaye na yankin da Israela ke son yi.

Ganin ranar daya ga wata mai kamawa da Israela ta tsayar don fara aiwatarda mamayan, ne daiduniya ke ta sukan shirin da nuna hadarin dake tattare da shirin wanda Amurka ta tsara.

Tsarin wanda shugaban Amurkan Donald Trump ya shirya dai, tuni Palestinawa suka yi fatali da shirin, inda Shugaban Hukumar kare ‘yancin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya ke ganin matakin zai yi matukar maida hannun agogo baya a kokarin wanzar da zaman lafiya mai dorewa a yankin Gabas ta Tsakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI