China-Hong Kong

Sabuwar dokar tsaron kasa a China ta haifar da cece-kuce

Kasashen Yammacin Turai sun bayyana shakku kan sabuwar dokar tsaron da China ta kafa a yankin Hong Kong.
Kasashen Yammacin Turai sun bayyana shakku kan sabuwar dokar tsaron da China ta kafa a yankin Hong Kong. AFP/Anthony WALLACE

Shugaban China Xi Jinping, ya rattaba hannu kan soma aikin sabuwar dokar tsaron kasa a Hong Kong, matakin da kasashen yammacin Turai ke kallo a matsayin hanyar kawo karshen kwarya-kwaryar yancin cin gashin kan da yankin ke da shi.

Talla

Jim kadan bayan rattaba hannu kan dokar tsaron, gwamnatin China ta bayyana ta a matsayin zararriyar takobi, dake kan duk wani mai barazana ga tsaron kasar.

Wani batu da ya dauki hankula shi ne yadda China ta ki bayyana abubuwa da dokar tsaron ta kunsa, lamarin da ya jefa mafi akasarin al’ummar yankin Hong Kong da yawansu ya kai miliyan 7 da rabi cikin fargaba gami da fusata.

Dokar da ba a baiwa majalisar Hong Kong damar tattaunawa a kai ba, ta soma aiki ne da yammacin wannan talata 30 ga watan Yuni, kamar yadda shugabar yankin Carrie Lam ta tabbatar.

Sai dai Amurka, Birtaniya, Kungiyar Tarayyar Turai, da kuma hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya, sun bayyana fargaba kan cewar gwamnatin China za ta iya amfani da dokar tsaron kasar wajen murkushe masu sukar ta, abinda ke nufin kawo karshen ‘yan adawa ta karfin tsiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI