Sai COVID-19 ta wuce za mu ci gaba da mamayar yankin Falasdinu- Isra'ila

Ministan tsaron Isra'ila Benny Gantz.
Ministan tsaron Isra'ila Benny Gantz. Adina Valman/Knesset Spokesperson's Office via Reuters

Ministan tsaron Isra’ila Benny Gants, ya ce kasar ba za ta ci gaba da mamayar yankunan Gabar Yammacin Kogin Jordan ba har sai an kawo karshen annobar covid-19 a kasar.

Talla

Da farko dai gwamnatin kawance karkashin jagorancin Benyamin Netanyahu, ta bayyana ranar 1 ga watan gobe na Yuli domin kaddamar da shirin fadada mamaye wasu yankuna da ke gabar yammacin kogin na Jordan mallakin Palasdinu.

To sai dai a cewar ministan tsaro Benny Gantz wanda ke jiran gadon Firaminista Netanyahu, lura da yadda dimbin mutane ke fama da cutar da coronavirus a kasar, a yanzu an jinkirta shirin na mamaya sai zuwa lokacin da aka yi nasara a kan cutar ta Covid-19.

Ofishin firaminista Netanyahu dai bai ce komai ba a game da wannan ikirari na Benny Gantz, wannan kuwa a daidai lokacin da kasahen duniya ke ci gaba da yin tir da kuma Allah wadai da sanarwar da gwamnatin ta Isra’ila ta fitar da ke cewa za ta mamaye karin yankunan Palasdinu, lamarin da ke matsayin babbar barazana ga shirin samar da zaman lafiya a yanking abas ta tsakiya.

Tuni dai Amurka ta bayyana cewa ba za ta iya hana Isra’ila aiwatar da wannan shiri nata ba, yayin da majiyoyi suka tabbatar da cewa a wannan litinin ma, an gana tsakanin Benny Gantz da manzon Amurka a yankin gabar tsakiya da kuma jakadan Amurka a birnin Tel Aviv kan wannan batu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.