China ta fara kamen masu kin mutunta sabuwar dokarta a Hong Kong
Fiye da mutane 300 jami’an ‘yansandan Hong Kong suka kame yau Laraba, cikinsu har da wadanda suka kalubalanci sabuwar dokar China wajen gudanar da kakkarfar zanga-zangar tunawa da zagayowar ranar da Birtaniya ta mika yankin mai kwarya-kwaryar ‘yanci ga China.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Wannan dai ne kamen farko da Chinan ta gudanar a yankin tun bayan kaddamar da dokar tsaron tata, wadda ta kara tsananta gangamin masu rajin kawo karshen mulkin mallakarta a yankin.
Karkashin sabuwar dokar ta yankin na Hong Kong dai China ta haramta gudanar da zanga-zanga don kawo karshen gangamin watanni da yankin ke fuskanta, sai dai da alamu sabuwar dokar naci gaba da yamutsa yankin wanda tun bayan kaddamar da dokar yake fuskantar boren jama’a.
Yayin zanga-zangar ta yau dai an samu arangama tsakanin fararen hula da jami’an tsaro wadda ta kai ga jikkatar da dama daga cikinsu, lamarin da ya sanya ‘yansandan kame mutane fiye da 200 kan laifin kalubalantar dokar da ta haramta gangamin, sai kuma wasu mutum 8 da aka kama na daban da laifin furta kalaman batanci da China baya ga muzanta taken kasar.
Yankin Hong Kong mai kwarya kwaryan ‘yancin, karkashin dokokin mika shi ga China da Birtaniya ta gindaya ranar 1 ga watan Yulin 1997, yana da cikakken ikon kan al’amuransa na shari’a da doka da oda ciki har da tsaro, matakin da masu zanga-zangar na yau ke ganin Chinar na neman wuce gona da iri batun da dama tuni ya ja hankalin kasashen duniya wadanda ke masa kakkausar suka.
Tuni dai Firaminista Boris Johson na Birtaniya da ya sha alwashin bayar da mafaka ga al’ummar yankin na Hong Kong ya ce a shirye ya ke ya basu shaidar zama cikakkun ‘yan Birtaniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu