Coronavirus-Gabas ta tsakiya

WHO ta yi gargadi kan tsanantar coronavirus a gabas ta tsakiya

Wasu al'ummar Iraqi karkashin matakan yaki da coronavirus.
Wasu al'ummar Iraqi karkashin matakan yaki da coronavirus. REUTERS/Thaier Al-Sudani

Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi gargadin cewar yankin gabas ta tsakiya na tsaka mai wuya dangane yadda su ke takaita dokar hana zirga-zirgar yaki da annobar coronavirus, a daidai lokacin da cutar ke yaduwa a yankin.

Talla

Daraktan Hukumar Lafiya dake kula da Gabas ta Tsakiya Ahmed al-Mandari ya ce yankin na su na cikin tsaka mai wuya dangane da yaduwar wannan annoba, wadda ke cigaba da lakume rayukan jama’a.

Hukumar lafiyar ta ce mutane sama da miliyan guda suka kamu da cutar coronavirus a yankin daga kasashe 22 da ofishin hukumar ke sanya ido akai, cikin su harda wasu dake Yankin Meditereniya.

Al-mandari ya ce sama da kahsi 80 na mutanen da suka mutu sakamakon kamuwa da cutar sun fito ne daga kasashe 5 da suka hada da Masar da Iran da Iraqi da Pakistan da kuma Saudi Arabia.

Hukumar tace alkalauman mutanen da suka kamu da cutar a watan Yuni kawai sun zarce wadanda suka samu a watanni 4 da suka gabata, abinda ke jefa fargaba ga jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.