Saudiya-Hajji

Saudiyya ta fara rajistar maniyyata aikin hajji 'yan kasashen ketare

Saudiya ta fara rajistar ‘yan kasashen ketare da aikin hajjin ya riske su a kasar don gudanar da aikin hajjin bana, tana mai cewa su ne za su kunshi kashi 70 na maniyyatar bayan ta dakile yawan maniyyatar sakamakon bullar annobar coronavirus.

Masallacin Kaaba.
Masallacin Kaaba. .REUTERS/Zohra Bensemra
Talla

Saudiyya ta ce maniyyata kimanin dubu guda da da aikin hajjin bana ya riske su a cikin kasarta ne kawai za ta bari su gudanar da aikin na wannan shekarar da zai gudana a watan Yulin nan da muke ciki, akasin mutane miliyan biyu da rabi da suka gudanar da aikin a shekarar da ta gabata.

‘Yan kasashen waje masu shekaru 20 zuwa 65, kuma wadanda ba su da tarihin cutar suga da ciwon zuciya ne aka yarje wa su yi wannan rajista da za a karkare ranar Juma’ar nan, kamar yadda ma’aiktar aikin hajji ta kasar ta sanar.

Ma’aikatar ta ce ‘yan asalin Saudiyya ne za su cike saura kashi 30 na maniyyatan da za su gudanar da aikin hajjin bana.

Za a yi wa wadannn maniyyata gwajin cutar coronavirus kafin su isa birnin Makka, kuma za a bukaci su killace kansu a gida bayan aikin.

Wannan ne karon farko a tarihi da Saudiyya ta dakatar da maniyyata daga wajen kasar gudanar da aiki hajji, lamarin da ya tada hankulan Musulmai a fadin duniya, sai dai da dama sun yi uzuri duba da ta’adin da cutar corona ke yi.

Mutane sama da dubu dari 2 da 13 ne suka harbu da wannan cuta a kasar, kusan 2000 suka ce ga garinku nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI