Faransa

Faransa ba ta shirin sake killace jama'a saboda coronavirus- Castex

Firaministan Faransa Jean Castex ya kawar da jita-jitar da ke nuna yiwuwar sake killace jama’ar kasar matukar aka fuskanci barkewar cutar coronavirus a karo na biyu.

Firaministan Faransa Jean Castex.
Firaministan Faransa Jean Castex. Thomas SAMSON / AFP
Talla

A cikin wata hira da ya yi da tashar talabijin ta BFM TV Firaministan na Faransa Jean Castex ya ce, ba za su dauki matakin sake killace mutane a gida kamar yadda aka yi a watan Maris da ya gabata ba.

A cewar Firaministan, Faransa ta gano illar da killacewar ke yiwa tattalin arziki da walwalar jama'a da ke tattare da sakamako mai radadi a don haka za su duba wasu hanyoyin na daban idan har annobar ta sake barkewa a karo na biyu.

Har ila yau Firaministan ya bayyana aniyarsa ta kai ziyara a jihar Guyane, jihar Faransa da ke da iyaka da kasar Brasil wadda ta harbu da annobar ta coronavirus.

Tuni dai aka aika karin ma'aikatan lafiya fiye da 130 zuwa jihar ta Guyane don tallafawa likitoci da ke aiki a yankuna daban-daban na tsibirin.

Kawo yanzu dai annobar coronavirus ta yi sanadiyar mutuwar kusan mutane dubu 30 a kasar ta Faransa, da a baya ta killace mutane a gida na tsawon watanni 2 tsakanin watanni Maris da mayu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI