Iran

Annobar COVID-19 ta gajiyar da ma'aikatan lafiyarmu - Iran

Ma’aikatar lafiyar Iran ya bayyana fargaba kan yadda annobar coronavirus ke dada yin karfi a kasar, la’akari da karuwar mutanen da take halakawa duk rana a kasar da kuma yawan wadanda suka kamuwa da cutar, yanayin da ta ce ba shakkah in ya ci gaba zai gajiyar da ma’aikatan lafiya.

Wasu ma'aikatan lafiya a Iran yayin kula da wani mai dauke ad cutar coronavirus
Wasu ma'aikatan lafiya a Iran yayin kula da wani mai dauke ad cutar coronavirus File/Reuters
Talla

A yau lahadi kadai, ma’aikatar lafiyar ta Iran ta ce rayukan mutane 216 annobar ta lakume, wanda kuma tun bayan sake barkewar cutar a karshen watan Yuni, kusan mako guda kenan, cutar na kashe sama da mutane 200 a kowace rana.

A halin yanzu akalla ma’aikatan lafiya dubu 5 suka kamu da cutar ta corona a Iran, daga cikin kusan mutane dubu 300 da suka kamu, yayinda kuma wasu dubu 15 da 700 suka mutu a kasar.

A makon jiya, 18 ga watan Yuli, shugaban Iran Hassan Rouhani ya kiyasta cewar mai yiwuwa yawan 'yan kasar da suka kamu cutar coronavirus ya kai miliyan 25, abinda ya sanya shi rokon da a dauke annobar da muhimmanci.

Rouhani yace a wani kyasin na daban, kimanin karin Iraniyawa miliyan 30 zuwa 35 ne cikin hadarin kamuwa da cutar ta coronavirus, kusan kashi 50 na yawan al’ummar kasar ta Iran mai yawan mutane miliyan 81 jumilla.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI