Korea ta Arewa

An sa dokar ta baci a koriya ta Arewa saboda Corona

Shugaban kasar Korea ta Arewa Kim Jong-Un.
Shugaban kasar Korea ta Arewa Kim Jong-Un. KCNA/via REUTERS

Rahotani daga Koriya ta Arewa na cewa hukumomin kasar sun rufe garin Kaesang da ke daf da iyaka da Koriya ta Kudu bayan sun samu mutum na farko da suke da yakinin ya harbu da cutar coronavirus.

Talla

Hukumomin kasar dai sun ce wani mutum da ya ketara zuwa Koriya ta Kudu shekaru 3 da suka wuce ne ya tsallako ba bisa ka’ida ba zuwa arewa, kuma yana nuna alamun cutar covid 19.

Idan aka tabbatar cutar corona ce yake dauke da ita, zai kasance karo na farko da aka samu mai cutar a kasar da ke da karancin kayan aiki a bangaren lafiya.

Kafin yanzu hukumomin kasar sun ce babu wanda ya harbu da wannan cuta, duk da cewa tana ta barna a kasashen da ke da ingattattun bangarorin lafiya kamar Amurka da Faransa da Jamus da Italiya.

Akalla mutane dubu dari 6 da 45 ne a fadin duniya wannan cuta ta kashe, yawancinsu daga Amurka da yankin Caribean.

Sai dai kwararu sun yi amannar cewa wannan cuta ta coronavirus ta dade da shiga Koriya ta Kudu daga China, inda ta samo asali, la’akari da kusancinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI