Isa ga babban shafi

Kotu ta sami tsohon Firaministan Malaysia da laifin cin dukiyar al'umma

Najib Razak, stohon Firaministan Malaysia
Najib Razak, stohon Firaministan Malaysia REUTERS/Lim Huey Teng
Zubin rubutu: Michael Kuduson
Minti 1

KOTU a kasar Malaysia ta sami tsohon Firaminista Najib Razak da laifuffuka 7 da aka tuhume shi da suka kunshi mallakar miliyoyin daloli shekaru biyu bayan zargin ya raba shi da mukamin sa.

Talla

Rahotanni sun ce samun sa da laifi a kan wannan zargi na iya haifar masa daurin shekaru akalla 35 a gidan yari bayan an tabbatar da laifi a kan sa na sace makudan kudade daga asusun ajiyar kasar.

Duk da kin amsa laifin sa mai shari’a Mohammed Nazian Mohammed Ghazali ya amince da shaidun da masu gabatar da kara suka gabatar masa na amfani da ofishin sa ta hanyar da bata kamata ba, da kuma azurtan kan sa da dukiyar jama’a da kuma halarta kudaden haramun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.