Iran

Mun kama shugaban kungiyar 'yan ta'adda mai cibiya a Amurka - Iran

Sashin Masallacin da aka kaiwa harin bam a birnin Shiraz dake kudancin kasar Iran. 12/4/2008
Sashin Masallacin da aka kaiwa harin bam a birnin Shiraz dake kudancin kasar Iran. 12/4/2008 AP Photo

Hukumomin tsaron Iran sun sanar da kame Jamshid Sharmad, shugaban kungiyar ‘yan ta’adda ta 'Tondar' da suka ce cibiyar ta ke Amurka.

Talla

Iran ta dade tana farautar ‘ya’yan kungiyar ta ‘yan ta’addan da suka kai harin bam a birnin Shiraz dake kudancin kasar, tare da ci gaba da yunkunrin kai wasu jerin hare-haren da jami’an tsaro a kasar ta Iran suka sha dakilewa.

Sanarwar hukumomin tsaron na Iran ba ta yi karin bayani kan lokaci da kuma inda suka kame Sharmahd ba, wanda ya shirya harin bam da ya kashe mutane 14, tare da jikkata wasu 215 a wani Masallaci dake birnin Shiraz ranar 12 ga watan Afrilun 2008.

A shekarar 2009, Iran ta zartas da hukuncin kisa kan 3 daga cikin ‘yan ta’addan da suke da hannu wajen kai farmakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI