Sri Lanka

'Yan sanda na farautar wata Kyanwa bisa tuhumar ta da safarar miyagun kwayoyi

Kyanwar da ake tuhuma da safarar miyagun kwayoyi a Sri Lanka.
Kyanwar da ake tuhuma da safarar miyagun kwayoyi a Sri Lanka. SRI LANKA POLICE/AFP via Getty Images

Jamian tsaro a kasar Sri Lanka sun kaddamar da farautar wata Kyanwa da a baya ake tsare da ita, saboda tarin laifuka, amma kuma ta tsere daga gidan Yarin Welikada da aka tsare ta.

Talla

Tun a ranar asabar 1 ga watan Agusta jami’an ‘yan sandan na Sri Lanka suka tsare Magen, bisa zargin ana amfani da ita wajen fasakwaurin miyagun kwayoyi da katunan wayan salula.

‘Yan sanda sun ce Kyanwar ta tsere ta barsu da sunki-sunkin miyagun kwayoyi da katunan salula da aka yi wasu dabaru aka makalawa mata a wuya.

A makwannin baya bayan nan jami’an gidan Yarin na Welikada suka bada rahoton yawaitar jefa musu kunshin miyagun kwayoyi, da wayoyin hannu ta katanga, da zummar isar da sakwannin ga wasu fursunoni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI