Amurka-Lebanon

Ba sinadarai bane suka haddasa tagwayen fashe-fashe a Beirut - Trump

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump AP Photo/Alex Brandon

A yayin da mahukunta a kasar Lebanon ke cewa ton dubu 2 da 700 na sinadarin Ammonium da ake amfani da shi don sarrafa takin zamani da sauran abubuwa masu fashewa ne suka haddasa fashewar da ta halaka sama da mutane 100 gami da jikkata wasu kusan dubu 400, a nasa bangaren, shugaba Donald Trump ya ce ya gana da wasu janar-janar na rundunar sojin Amurka da suka sanar da shi cewa fashewar “ta yi kama da bama-bamai’’

Talla

Trump ya ce sojojin sun sanar da shi cewar fashewa ba ta yi kama da sinadiran da ake amfani da su a cikin masana’antu ba, inda ya ce lamarin ya yi kama da harin bam ko kuma wani abu mai kama da haka.

Yanzu haka dai kasashen duniya na ci gaba da nuna alhini a game da wannan lamari, inda shugabannin kasashe da suka hada da na Faransa Emmanuel Macron, Vladimir Putin na Rasha, da na Firaminsitan Birtaniya Boris Johnson, da kuma Justin Trudeau na Canada na cikin wadanda suka bayyana matukar kaduwarsu a game da wannan lamari.

Hakazalika sakataren wajen Amurka Mike Pompeo da ministan tsaron Isra’ila Benny Ganz sun isar da irin wannan sako na ta’aziya ga al’umar Libanan, kamar dai yadda aka samu irin wadannan sakonni daga kasashen yankin Gulf da suka hada da Qatar, Kuwait, da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI