Kayayyakin agaji na kasa-da-kasa sun fara isa Beirut

Kayakin agaji na kasa da kasa sun fara isa Lebanon
Kayakin agaji na kasa da kasa sun fara isa Lebanon REUTERS/David W Cerny

Kayayyakin agaji gaggawa, musamman na kula da lafiya da suka hada da asibitocin tafe – da – gidanka, gami da kwararru kan aikin ceto, har ma da karnuka masu shinshina sun isa Lebanon a Laraba nan, yayin da kasashen duniya ke ribibin kai dauki ga wadanda fashewar wani abu ya rutsa da su a Beirut.

Talla

Fashe fashen da suka auku a tashar jiragen ruwan kasar ta Lebanon, sun haifar da gagarumar barna da ta yi sanadin mutuwar mutane sama da 100, lamarin da ya ta’azara rikici a kasar da ke fama da rikice rikice iri dabam dabam da suka hada da annobar coronavirus.

Kayayyakin kula da lafiya daga Kuwait sun isa Beirut, babban birnin Lebanon a Laraban nan, yayin da kungiyar agaji ta Red Cross a kasar ke cewa suna yi wa sama da mutane dubu 4 magani sakamakon raunin da suka samu a wannan mummunar al’amari.

Kasashen yankin tekun Fasha na sahun gaba cikin kasashen da suka kai dauki wannan kasa da ta gamu da iftila’in fashe fashe, bayan da Firaministan Lebanon Hassan Diab ya yi kira ga abokan hulda da su kawo dauki, don samar wa kasar da ke fama da matsin tatalin arziki sauki.

Kasashen duniya da dama sun yi ta mika sakonnin jaje ga Lebanon bisa wannan mummmunar al’amari da ya same ta, tare da alkawarin gudummawar kayayyakin da ake bukata, inda shugaban Iran Hassan Rouhani ke baayyana shirin kasarsa na taimakawa wajen yi wa wadanda suka ji rauni magani, haka ma Sarkin Jordan, Abdallah Na 2.

Yayin da ake ci gaba da zakulo wadanda suka makale a baraguzan gine gine, Faransa ta ce ta aike da kwararru masu aikin ceto tare da dimbim kayyakin agaji zuwa Lebanon.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI