Sake gina wurin bautar Hindu a Ayodhya ya janyo cece-kuce a India

Firaministan India Narendra Modi, yayin kafa tubalin gina sabon katafaren wurin bautar mabiya addinin Hindu a birnin Ayodhya mai tarihi,
Firaministan India Narendra Modi, yayin kafa tubalin gina sabon katafaren wurin bautar mabiya addinin Hindu a birnin Ayodhya mai tarihi, SANKET WANKHADE / AFP

Firaministan India Narendra Modi ya bayyana kafa muhimmin tarihi a yau Laraba, a daidai lokacin da ya kafa tubalin gina sabon katafaren wurin bautar mabiya addinin Hindu a birnin Ayodhya mai tarihi, dadadden wajen bautar da ya sha haddasa kazamin rikicin addini a kasar.

Talla

Gagarumin bikin kafa harsashin ginin sabon wurin bautar na addinin Hindu, ya zo daidai da zagayowar ranar da gwamnatin Firaminista Modi ta soke kwaryakwaryar yancin da yankin Kashmir dake karkashin ikon India ke amfana da shi, yankin da yafi rinjayen Musulmi a kasar.

A bangaren magoya bayansa mabiya addinin Hindu, tsauraran matakan biyu da Modi ya dauka sun tabbatar masa da matsayin zama tsayayyen jagora, jarumi mai kuma hangen nesa.

Yayinda bangaren masu adawa, ke kallon Firaministan na India a matsayin mutumin dake sauya alkibilar India daga kasa mai yawan mutane biliyan 1 da miliyan 300 da babu ruwanta da addini zuwa kasar mabiya addinin Hindu don tauye hakkin Musulmin kasar miliyan 200, da kuma rikidewa zuwa shugaba mai mulkin kama karya.

A shekarar 1992, gungun mabiya addinin Hindu suka rusa wani Masallaci da aka shafe sama da shekaru 400 da gina shi a birnin Ayodhya mai tarihi, wanda suka ce an gina shi ne kan wurin da aka haifi abin bautarsu Ram, lamarin da ya haifar da kazamin rikicin addinin da ya lakume rayukan akalla mutane dubu 2, mafi akasarinsu Musulmi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI