Jami'an tsaro sun tarwatsa masu zanga-zangar adawa da gwamnati a Beirut

Jam'an tsaro sunyi amfani da hayaki mai sa kwalla kan masu zanga-zanga a Beirut
Jam'an tsaro sunyi amfani da hayaki mai sa kwalla kan masu zanga-zanga a Beirut Reuters

‘Yan sandan kwantar da tarzoma a kasar Lebanon sun harba hayaki mai sa hawaye kan dandazon masu zanga-zangar da sukayi kokarin karya shingen shiga majalisar dokokin kasar dake tsakiyar Beirut.

Talla

Sabuwar zanga-zangar adawa da gwamnati na zuwa ne kwanaki biyar bayan wasu abubuwa masu fashewa sunyi sanadiyar mutuwar mutane sama da 150 akasarisu ‘yan kasar Syria, yayin da wasu sama da dubu 6 suka jikkata, kana sama da mutene dubu 300 suka rasa muhallansu.

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kasashen Duniya su mayar da hankali ga kasar Lebanon, tareda bayar da agaji da zai taimaka don rage radadin da yan kasar ke fama da shi bayan fashewar da ta wakana ranar Talata a Beirut.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI