Afghanistan zata sallami fursunonin Taliban 400
Wallafawa ranar:
Gwamnatin Afghanistan tace ana daf ta fara zaman Tattaunawar zaman lafiya mai dinbin tarihi tsakaninta kungiyar Taliban, bayan babban taron kwamitin zaman lafiyar kasar ya amince da sakin fursunonin Taliban 400 ci harda masu manyan laifuka.
Shugaban kwamitin dake da alhakin jagorantar tattauwar Abdullah – Abdullah ya bayyana wannan mataki, inda yace ana gaf da fara tattaunawar da zaran an sallami mayakan na Taliban dake tsare.
Tsohon Shugaban kasar Hamid Karzai ya ce akai tabbacin soma tattaunawar nan da kwana daya ko biyu, bayan sakin fursunoni 400."
Itama kasar Amurka ta bakin Sakataren Tsaron ta Mike Esper yace zasu rage yawan dakarun su dake aiki a kasar Afghanistan nan da watan Nuwamba mai zuwa, inda zasu bar kasa da 5,000.
Wannan na zuwa ne bayan sanarwar da shugaba Donald Trump ya gabatar cewar zasu rage dakaru 4,000 daga cikin 8,600 da yanzu haka ke cikin kasar ta Afghanistan.
Janye dakarun Amurka daga Afghanistan na daga cikin yarjejeniyar da kungiyar Taliban ta kulla da wakilan a Amurka a yunkurin kawo karshen tashin hankalin da ake samu a Afghanistan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu