Lebanon

Firaministan Lebanon ya yi murabus

Hassan Diab, Firaministan Lebanon.
Hassan Diab, Firaministan Lebanon. Mohamed Akazir/Reuters

Firaministan Lebanon, Hassan Diab ya yi murabus biyo bayan tayar da jijiyar wuya a ciki da wajen gwamnatinsa, sakamakon mummunar fashe fashen sinadarai a tashar jiragen ruwan Beirut.

Talla

Firaminista Hassan Diab, a wani jawabi da ya yi ga al’ummar kasar ya ce ya zama wajibi ya yi aiki da muradan al’ummar kasar, saboda haka yake sanar da cewa gwamnatinsa ta yi murabus.

A game da fashe fashen da suka auku a ranar 4 ga watan Agusta kuwa, Diab, ya zargi rukunin ‘yan siyasa da suka mulki kasar tsawon shekaru 30 da zama ummu’abaisan faruwar lamarin.

Jagororinn yakin basasar Lebanon na tsakanin shekarun 1975 zuwa 1990, wadanda suka tube kaki, ko ‘yan uwansu ne suka mamaye siyasar kasar, kuma sune Diab yake zargi da rashawa da ta jefa kasar cikin mummunar yanayi.

Masu sukar gwamnatin Lebanon dai sun danganta halin da kasar ke ciki da rashin sanin makaman aiki da rashawa da suka mamaye gwamnati mai mulkin kasar.

Diab wanda ya dare karagar mulki a watan Disambar bara, shine firaministan Lebanon na biyu da ya yi murabus a cikin watanni 10.

Gwamnatinsa da aka kafa watan Janairu don ta dakile matsalar tattalin arziki da kasar ke fuskanta ta fuskanci zanga zangar gama – gari sakamakon fashe fashen da suka yi sanadiyar mutuwar mutane 160, suka kuma jikkata dubu 6.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.