Isra'ila

Dubban 'yan Isra'ila na zanga-zangar neman Netanyahu ya yi murabus

Dubban 'yan Isra'ila a birnin Kudus yayin zanga-zangar neman Firaminista Netanyahu ya yi murabus
Dubban 'yan Isra'ila a birnin Kudus yayin zanga-zangar neman Firaminista Netanyahu ya yi murabus Olivier Fitoussi/Flash90

Dubban ‘yan Isra’ila sun sake fita kan titunan birnin Kudus, inda suke zanga-zangar neman murabus din Firaministan kasar Benjamin Netanyahu, bisa zarginsa da laifukan rashawa, da kuma gaza daukar matakan dakile yaduwar annobar coronavirus.

Talla

Rahotanni sun ce tun cikin daren ranar asabar, aka soma samun arrangama tsakanin masu zanga-zangar da jami’an tsaro, lamarin da ya cigaba zuwa wayewar garin yau lahadi, a gaf da gidan Firaminista Netanyahu.

Mako na 8 kenan da dubban ‘yan Isra’ila ke gudanar da zanga-zangar ta kin jinin Netanyahu.

Hotunan da aka wallafa a shafukan Internet sun nuna yadda ‘yan sanda ke jan masu zanga-zangar da suka damke, bayan hana su yin tattaki zuwa cikin harabar Firaministan na Isra’ila.

Jaridar Haaretz dake kasar tace yawan masu zanga-zangar da suka fita a biranen kasar ranar Asabar, ya kai dubu 50.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.