Tagwayen fashe fashe sun kashe mutane 10 a Philippines

Taswirar da ke nuna tsibirin Philippines.
Taswirar da ke nuna tsibirin Philippines. @Wikipedia

Akalla mutane 10 sun mutu da dama suka samu raunuka ciki har da sojoji da ‘yan sanda a yau Litinin a wasu tagwayen hare hare a kudancin tsibirin Philippines.

Talla

Harin ya auku ne a yankin Jolo, yankin da Musulmi ‘yan kabilar Sulu suka fi rinjaye, inda dakarun gwamnati suka dade suna gumurzu da kungiyar Abu Sayyaf.

Sojoji 5 da farar hula 4 suka mutu a fashewar farko, yayin da wani bam da aka jona da wani babur ya tarwatse a wajen wani katafaren shago.

Sojoji 16 da Kimanin fararen hula 20 ne suka jikkata a fashe fashen  da suka suka auku a tsakiyar dare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.