Isa ga babban shafi

An rantsar da Mustapha Adib, a matsayin sabon Firanministan Lebanon

Moustapha Adib sabon Franministan Lebanon
Moustapha Adib sabon Franministan Lebanon REUTERS/Mohamed Azakir
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman | Ahmed Abba
Minti 2

Shugabannin siyasar Lebanon sun zabi masanin sha’anin diflomasiya Mustapha Adib, a matsayin sabon Fira Minista, abinda suke fatan zai kawo karshen rikicin siyasa da matsalar tattalin arzikin da a yanzu kasar ke ciki.Zaben na zuwa ne sa’o’i kafin soma ziyarar da shugaban Faransa Emmanuel Macron a kasar ta Lebanon a Talatar nan dake tafe. 

Talla

Yayin jawabin sa na farko da ya gabatar bayan shan rantsuwar kama aiki, sabon firanministan na Lebanon Mustafa Adib, yace ba shakkah akawai bukatar yin garambawul ga tsarin shugabancin kasar kafin ya kafa sabuwar gwamnati, matakan da ya sha alwashin soma aiwatarwa nan take.

Adib ya kuma ce zai gaggauta cigaba da tattaunawa da asusun bada lamuni na duniya IMF, dangane da bukatar baiwa Lebanon tallafin farfado da tattalin arzikinta da ya durkushe, musamman bayan tagwayen fashe-fashen da suka auku a tashar ruwan Bierut da suka auku a ranar 4 ga watan Agustan nan mai karewa, abinda ya kai ga rasa dimbin rayuka da kuma tafka hasarar sama da dala biliyan 5.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da ya kai ziyarar gaggawa zuwa birnin Bierut kwanaki 2 bayan fashe-fashen zai sake ziyartar kasar karo na biyu nan da sa’o’i, inda ake sa ran zai gana da sabon fira minister Mustapga Adib da aka zaba, kan bukatar sauya fasalin shugabancin kasar ta Lebanon, kudurin da ya samu goyon bayan shugaban kasar Michel Aoun da jagoran kungiyar Hezbollah Hassan Nasrallah.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.