China ta dawo da sufurin jiragen saman kasa-da-kasa bayan korona

Yadda aka fara jigilan fasinjoji a filin sufurin jiragen saman kasa-da-kasa a China
Yadda aka fara jigilan fasinjoji a filin sufurin jiragen saman kasa-da-kasa a China REUTERS/Benoit Tessier

Bayan share tsawon watanni 5 da rabon manyan biranen kasar China da tashi da saukar jiragen saman kasa da kasa saboda yaduwar annobar covid-19. A yau Alhamis kasar ta sake bude sauka da tashin jiragen kasashen duniya a birnin Pékin..

Talla

Birnin Pékin ya zama sabon birnin da aka sake budewa harkokin sauka da tashin jiragen sama a duniya, bayan share tsawon kwanaki 164 da rabon sararin samaniyarsa da zirga zirgar jiragen kasashen na ketare.

Jirgin farko da ya sauka a yau alhamis ya fito ne daga Phnom Penh na kasar Kambodjiya, da bangaren yawon buda idon kasar ta china ya jima yana jiran ganin faruwarsa, wanda kuma wani bangaren alúmmar birnin na Pekin ke kallo a matsayin sake dawowar lamurra dai dai a wannan fanni na sufurin jiragen kasa da kasa.

Kusan za a iya cewa dai, tun ranar 26 ga watan ogustan da ya gabata rabon birnin na China ya samu mutum daya da ya kamu da anobar ta Covid-19, wannan gwaji da mahukumtan kula da tashi da saukar jiragen saman kasar ta china suka sanar, zai kasance kasance ne a takaice ga wasu kasashen duniya dake da ake samun karancin wadanda ke kamuwa da annobar a halin yanzu.

Kasashen da suka hada da: Thaïlande, Cambodge da kuma Pakistan a nahiyar ’Asiya, sai kuma Grèce, Danemark, Autriche da Suède a nahiyar turai, da kuma kasar Canada dake yankin nahiyar Amruka ta arewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.