Pakistan-Faransa

Al'ummar Pakistan na zanga-zangar kin jinin Faransa kan zanen batanci ga Annabi

Zanga-zangar ta yau, na gudana ne karkashin jagorancin babbar jam’iyyar kasar mai rajin kare maradan addinin Islama wato Tahreek-e-Labbaik Pakistan.
Zanga-zangar ta yau, na gudana ne karkashin jagorancin babbar jam’iyyar kasar mai rajin kare maradan addinin Islama wato Tahreek-e-Labbaik Pakistan. REUTERS/Akhtar Soomro

Dubban musulmai ne yau juma’a suka fara zanga-zangar kin jinin Faransa a Pakistan don nuna bacin rai kan zanen batancin da mujallar barkwanci ta Charlie Hebdo ta fitar da ke matsayin batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammadu tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gareshi.

Talla

Tun bayan fitar mujallar ta mako mako ne Ma’aikatar wajen Pakistan ta yi tir da matakin yayinda jagororin addinin Islama suka fara kiraye-kirayen gudanar da gangamin da aka tsara aiwatar da shi bayan sakkowa daga sallar juma’a a yau.

Tuni dai Pakistan mai rinjayen mabiya addinin Islama ta sanar da korar jakadun Faransar yayinda ta fara daukar matakin yanke hulda baya ga kauracewa harkokin cinikayya.

A farkon makon nan ne jaridar ta Charlie Hebdo ta sake fitar da zanen dai dai lokacin da za a fara shari’ar maharan 2015, harin da ke da alaka ta kai tsaye da fitar makamancin zanen a shekarun 2005 da 2006 wanda ya haddasa yamutsi da tsamin alaka tsakanin Faransar kasar da mujallar ta ke da duniyar musulmi.

Wani guda cikin jagororin masu zanga-zangar da aka bayyana sunanshi da Muhammad Ansari cikin bacin rai ya bayyana cewa sam Musulmi baza su lamunci rashin da’ar mujallar na batanci ga fiyayyen halitta mafi soyuwa a zukatan musulmi fiye da komi ba.

Bisa ka’idojin addinin Islama dai fitar da wani hoto ko zane tare da bayyana shi a matsayin Annabin rahamar fiyayyen halitta tsira da amincin Allah su tabbata a garsehi na matsayin haramtaccen al’amari yayinda hukunci kan aikata hakan a wasu kasashen musulmi ciki har da Pakistan ke matsayin kisa har lahira.

Zanga-zangar ta yau, na gudana ne karkashin jagorancin babbar jam’iyyar kasar mai rajin kare maradan addinin Islama wato Tahreek-e-Labbaik Pakistan, Jam’iyyar da ta yi kaurin suna wajen jajircewa don ganin an tafiyar da al’amura bisa tanadin addinin Islama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.