Korea ta Arewa

Ambaliyar ruwa ta rusa gidaje da dama a Koriya ta Arewa

Shugaba Kim Jong-un na Korea ta Arewa.
Shugaba Kim Jong-un na Korea ta Arewa. KCNA via REUTERS

Shugaban Koriya ta arewa Kim Jong Un ya umurci wasu wakilan jam’iyar sa mai mulki 12.000 da su dau harami don isa yankunan da aka fuskanci amballiya da nufin dafawa wajen sake gina yankunan tareda kai dauki ga mabukata mazauna wadanan wurare.

Talla

A jiya asabar Shugaban Koriya ta arewa Kim Jong Un bayan ziyarar da yake yankunan da ruwa suka yi gyara, nan take ya dau mataki na tube kantoman yankin Hamgyong ta kudu.

A shekara ta 2016,yan koriya ta arewa 138 ne suka mutu sannadiyar ambaliya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.