Hong Kong

'Yan sandan Hong Kong sun kame kusan mutane 300 yayin sabuwar zanga-zanga

wasu daga cikin masu zanga-zangar da 'yan sandan Hong Kong suka kama.
wasu daga cikin masu zanga-zangar da 'yan sandan Hong Kong suka kama. AFP

Yan sandan kwantar da tarzoma a Hong Kong sun kame kusan mutane 300, yayin zanga-zangar da dubban al’ummar yankin ta yau lahadi, biyo bayan dage zabukan da gwamnatin yankin ta yi.

Talla

Yau lahadi ne daia aka tsara zabukan na Hong Kong za su gudana amma shugabar yankin carrie Lam ta sanar da dage su da tsawon shekarar 1, saboda annobar coronavirus.

Sai dai matakin ya fusata mafi akasarin al’ummar yankin, musamman ‘yan adawar dake fafutukar sauya tsarin mulkinsu zuwa dimokaradiyar yammacin Turai.

‘Yan gwagwarmayar assasa dimokaradiyya da dama ne hukumomi a Hong Kong suka haramta wa tsayawa takara a zaben ‘yan majalisun dokokin yankin dake tafe a watan Satumba mai zuwa, matakin da ‘yan takaran suka bayyana a matsayin cin zarafin masu sukar gwamnatin China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.