India-Coronavirus

India ta zama kasa ta biyu mafi yawan masu dauke da coronavirus

Wasu jami'an lafiya a India.
Wasu jami'an lafiya a India. REUTERS/P. Ravikumar/File Photo

India ta wuce gaban Brazil a yawan masu dauke da coronavirus inda yanzu ta dawo ta biyu a yawan masu dauke da cutar kaf duniya, duk da cewa tuni kasar ta dawo da wasu harkokin hada-hada ciki har da zirga-zirgar jiragen kasa a wani yunkuri na dakile kalubalen tattalin arzikin da ke tunkarota.

Talla

A baya-bayan nan ne India ta zamo mafi samun sabbin kamuwa da cutar inda ta ke samun sabbin kamuwa akalla dubu 91 kowacce rana da jumullar mutum miliyan 4 da dubu dari 2 yanzu haka masu dauke da cutar wanda ke nuna Amurka ce kadai mai jumullar masu coronavirus miliyan 6 da dubu dari 2 ke gaban Indiar.

Baya ga India sauran kasashen da ke fuskantar yawaitar sabbin kamuwa da cutar ta coronavirus a baya-bayan nan sun hadar da Faransa, Isra’ila da kuma Australia, dai dai lokacin da duniya ke da jumullar mutum miliyan 27 da cutar ta kama ciki har da mutane dubu 880 da ta kashe a sassa daban-daban.

A yau litinin ne India ta sanar da dawowar zirga-zirgar jiragen kasar bayan dakatar da su na tsawon watanni biyar don dakile cutar ta coronavirus, inda tuni hada-hadar ta fara kankama a New Delhi da wasu manyan birane 12 sai dai karkashin matakan kariya daga cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI