Gabas ta tsakiya

Sabuwar huldar diflomasiya tsakanin Isra'ila da kasashen Larabawa

Firaministan Isra'ila  Benyamin Netanyahu tareda Sarkin  Bahreïn Hamad bin Isa al-Khalifa
Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu tareda Sarkin Bahreïn Hamad bin Isa al-Khalifa RONEN ZVULUN, Fayez Nureldine / AFP

Kamfanin sufurin jiragen sama na Isra’ila ya baayyana shirinsa na fara jigilar fasinjoji daga Tel Aviv zuwa Abu Dhabi kai tsaye bayan da Israila da Hadaddiyar daular Larabawa suka amince da maido da dangantaka a tsakaninsu.

Talla

Isra’ila da da Hadaddiyar Daular Larabawan sun shirya tsaf don sanya hannu a daftarin yarjejeniya a fadar White House ta kasar Amurka,

Indan aka yi tuni tun a ranar 6 ga watan Disemba na shekara ta 2017 da Shugaban Amurka Donald Trump ya amince da birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar ta Isra’ila ne aka soma tattaunawa ta bayan fage da wasu kasashen Larabawa don sake dawo da hulda a tsakanin su,huldar da wasu daga cikin kasashen Larabawa suka yi tir da Allah wadai.

Iran ta bayyana damuwa tareda yin tir da Allah wadai da wannan mataki da aka cimma tsakanin Isra'ila da wadannan kasashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.