Japan

Suga ne zai zama sabon Firaministan Japan

Yoshihide Suga, wanda ya shirya tsaf don darewa kujerar Firaministan Japan kwanan nan.
Yoshihide Suga, wanda ya shirya tsaf don darewa kujerar Firaministan Japan kwanan nan. REUTERS/Kim Kyung-Hoon

Babban sakataren majalisar ministocin Japan, Yoshihide Suga, ya shirya tsaf dan darewa kujerar Firaministan kasar bayan da jam’iyya mai mulki ta zabe shi a matsayin wanda zai gaji Firaminista mai barin gado, Shinzo Abe.

Talla

Cikin ruwan sanyi Suga ya samu kuri’u 377 daga cikin 534 da ’yan majalisar dokokin daga jam’iyyar Liberal Democratic Party suka kada, inda ya baiwa abokan hamayyarsa biyu rata.

Duba da cewa jami’iyyarsa ce ke da rinjaye a majalisar dokokin kasar Japan, ana ganin ba makawa zai samu galaba idan aka je kada kuri’a a majalisar a ranar Laraba mai zuwa, don zabo magajin Shinzo Abe, wanda yayi murabus bisa dalilin rashin lafiya.

Yayin jawabin amincewa da zabensa da jam’iyyarsa ta yi, Toshihide Suga mai shekaru 71, ya sha alwashin ci gaba da manufofin firaminista mai barin gado Abe, da zummar shawo kan matsalolin da ke addabar al’ummar kasar.

Tun kafin ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a hukumance, dan shekara 71 ya samu goyon bayan manyan bangarori na jam’iyyar, inda ake ganin takarar tasa a matsayin abin da zai kawo wa kasar nutsuwa.

A kuri’ar da aka kada, Suga ya doke tsohon ministan tsaron kasar, Shigeru Ishiba da shugaban tsara manufofin jami’iyyar ta LDP Fumio Kishida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.