India

Rushewar bene ta kashe mutane da dama a India

Wurin da aka samu ibtila'in rushewar gini a  Bhiwandi na India
Wurin da aka samu ibtila'in rushewar gini a Bhiwandi na India Reuters

Hukumomin India sun ce, mutane 10 suka mutu sakamakon rushewar wani bene mai hawa 3, yayin da ake fargabar cewar ginin ya danne wasu karin mutane 25 a cikinsa.

Talla

Rahotanni sun ce, an samu hadarin ne a birnin Bhiwandi da ke makotaka da birnin Mumbai, kuma yanzu haka jami’an agaji na ci gaba da gudanar da aikin ceto.

Darakta Janar na hukumar agajin gaggawa Satya Narayan Pradhan ya ce, jami’an na dauke da na’urorin zamani da kuma karnuka domin ceto sauran mutanen.

Kawo yanzu babu cikakken bayani game da musabbabin ruftawar ginin, amma gine-gine na yawan rushewa musamman tsakanin watannin Yuni zuwa Satumba a India.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.