Tsarin wasannin gasar Olympics cikin korona

Hukumar shirya gasar wasannin Olympics ta Tokyo 2020 sun fitar da tsarin wasannin a shekara mai zuwa
Hukumar shirya gasar wasannin Olympics ta Tokyo 2020 sun fitar da tsarin wasannin a shekara mai zuwa REUTERS/Issei Kato

Masu shirya gasar wasannin Olympics ta Tokyo da aka jinkirta zuwa shekara mai zuwa saboda barkewar annobar korona, sunce za a bukaci gwajin kwayar cutar ga ‘yan wasa daga kasashen waje da zarar isarsu Japan, to amma mai yiwuwa ba za a bukaci killacewar makonni biyu.

Talla

Cikin rahoton da kwamitin shirya gasar ta Tokyo 2020 ya fitar jiya Talata, bayan ganawa da gwamnatin Japan da hukumomin babban birnin Tokyo, ya kuma nuna cewa wannan mataki zai shafi, ’Yan wasan gujeguje da tsalle-tsalle na cikin gida Japan da sauran mahalarta da ke zaune a cikin kasar, a lokutan zuwa sansanonin atisaye da kuma filayen gasar.

Annobar korona wacce ta kama miliyoyin mutane a fadin duniya, ta jefa fargaba kan yiwuwar shirya Wasannin a badi, ko da yake, sabon Firayim Ministan Japan Yoshihide Suga ya jaddada mahimmancin gasar.

A safiyar jiya Laraba, Suga ya yi magana da Shugaban Kwamitin Gasar na Duniya Thomas Bach ta wayar tarho kuma ya tattauna game da gudanar da Wasannin cikin nasara.

Suga ya yi alkawarin bada hadin kai domin samun gudanar gasar mai inganci da tsanaki, tare da kare lafiyar 'yan wasa da' yan kallo, in ji ofishinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.