China-Coronavirus

China za ta samar da maganin Covid-19 dubu 600 kafin karshen shekara

Wani dakin gwajin maganin cutar ta Covid-19 a China.
Wani dakin gwajin maganin cutar ta Covid-19 a China. NOEL CELIS / AFP

Kamfanin harhada magunguna na China da ke aikin samar da maganin cutar Covid-19 ya sanar da shirin samar da magungunan fiye da miliyan 600 zuwa nan da karshen shekara, dai dai lokacin da adadin mutanen da cutar ta halaka a sassan duniya ya kai dubu 984.

Talla

China da ke sanar shirin samar da maganin miliyan 610 yayin wani taron manema labarai yau a Beijing da ya kunshi kwararru a bangaren lafiyar kasar da kuma bangaren harhada magunguna, ta ce zuwa shekarar 2021 kamfanonin kasar da ke aikin samar da maganin na Covid-19 za su samu damar fitar da magungunan akalla miliyan guda.

Zuwa yanzu kamfanonin China, 11 suka shiga sahun manyan kamfanonin harhada magunguna na duniya a kokarin samar da maganin cutar ta Cvid-19 da kawo yanzu ta hallaka mutum dubu 984 da 68 a sassan duniya.

A cewar shugaban ma’aikatar kimiyya da fasaha na Chinan, Wu Yuanbin zuwa yanzu kamfanonin kasar 3 sun tsallake gwajin karshe na shirin samar da maganin yayinda 4 ke gab da rukunin karshe sai kuma sauran 4 da ke matakin farko, duk dai a kokarin wadata duniya da maganin cutar ta Covid-19.

cewar Mr Wu yanzu haka kamfanonin na China 3 su ne sahun gaba a duniya ta fuskar ka iwa matakin gab da karshe a kokarin samar da maganin na Covid-19.

Majiyar Lafiya a Chinan ta sanar da yadda mutane da dama suka fara karbar gwajin maganin tun tsakiyar watan Yuli a sassan kasar ta China bisa sahalewar Majalisar Dinkin Duniya, yayinda Shugaba Xi Jinping ke sake shelanta shirin kasar na ganin ta wadata duniya da maganin cutar ba tare da fifita wani yanki ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.