China

Hukumomin China sun rusa Masallatai sama da dubu 15 a Xinjiang - Rahoto

Wasu Musulmi yayin gabatarda Sallah a daya daga cikin Masallatan dake yankin Xinjiang a kasar China.
Wasu Musulmi yayin gabatarda Sallah a daya daga cikin Masallatan dake yankin Xinjiang a kasar China. Greg Baker / AFP

Wata cibiyar bincike kan lamurran yau da kullum mai zaman kanta dake kasar Australia ASPI, tace gwamnatin China ta rusa dubban Masallatai a yankin Xinjiang.

Talla

Rahoton da cibiyar ta ASPI ta wallafa a yau Juma’a shi ne na baya bayan nan daga cikin jerin rahotanni da kungiyoyin kare hakkin da adam kan yadda hukumomin kasar ta China ke cin zarafin Musulmi da ma sauran kabilu marasa rinjaye a yankin na Xinjiang.

Cibiyar ta ASPI tace ta tattara bayananta ne ta hanyar amfani da hotuna daga tauraron dan adam da suka nuna cewar hukumomin na China sun rusa kimanin Masallatai dubu 16 a yankin na Xinjiang a tsawon shekaru 3 da suka gabata.

Sabon rahoton ya kara da cewar babu wani wurin ibada na mabiya addinin Buddah ko kuma Mujami’u da hukumomin na China suka taba, yayinda suka rushe akalla kashi 1 bisa 3 na wuraren ibada na Musulmi, musamman biranen Urumqi da Kashgar da ke yankin na Xinjiang.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun dade suna zargin hukumomin China ta tsare Musulmi ‘ yan kabilar Uighur da Turkic sama da miliyan 1 a wasu sansanoni da ke arewa maso yammacin kasar da nufin tilasta musu barin addini da kuma al’adunsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.