Lebanon

Sabon fira ministan Lebanon yayi murabus

Sabon fira ministan kasar Lebanon da yayi murabus a kasa da wata 1, Mustapha Adib.
Sabon fira ministan kasar Lebanon da yayi murabus a kasa da wata 1, Mustapha Adib. File/AFP

Sabon fira ministan Lebanon Mustapha Adib yayi murabus kasa da wata guda bayan nada shi kan mukamin.

Talla

Ranar 31 ga watan Agustan da ya gabata, manyan jagororin Lebanon suka amince da nada Adib a matsayin fira ministan da aka dorawa alhakin kafa sabuwar gwamnati, da za ta maye gurbin wadda ta yi murabus, bayan aukuwar fashe-fashen sinadaran ammonium a tashar jiragen ruwan Beirut ranar 4 ga watan na Agusta, da suka yi sanadin mutuwar akalla mutane 190.

Sai dai cikin a yau asabar 26 ga Satumba Mustapha Adib ya bayyana ajiye mukaminsa, gami da neman gafarar al’ummar Lebanon bisa gazawar da yayi na sauke nauyin da aka dora masa.

Ko da yake Adiba bai bayanna dalilan da suka sanya shi yin murabus din na bazata ba, majiyoyi masu tushe sun ce matakin na da nasaba da yadda manyan jam’iyyun siyasar kasar na Amal da Hezbollah suka ki amincewa da wasu bangarorin shirin sabon fira ministan na kafa sabuwar gwamnati, inda takaddama ta barke kan bangaren da ya cancanci rike madafun ikon ma’aikatar kudin kasar.

Tun kafin aukuwar fashe-fashen watan Agusta, Lebanon ke fama da matsalar tattalin arziki, mafi muni da ta gani tun bayan na shekarun 1975 zuwa 1990, lokacin yakin basasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.